Boko Haram ta sako ma’aikatan agaji su biyar


Mayakan kungiyar Boko Haram sun sako wasu ma’aikatan kungiyoyin agaji da suka yi awon gaba da su.

An yi garkuwa da ma’aikatan agajin ne su biyar a jihar Borno.

Wasu majiyoyi na jami’an tsaro sun tabbatarwa da jaridar The Cable cewa an sako mutanen ranar Laraba.

Wata majiya dake hukumar tsaron farin kaya DSS ta tabbatarwa da jaridar sako mutanen bayan tattaunawa da mayakan kungiyar sai dai jaridar ta gaza tabbatarwa ko an biya kudin fansa kafin a sako mutanen.

Ma’aikatan agajin maza biyu da kuma mata uku an sace su kwanaki uku kafin ranar Kirsimeti. Mayakan Boko Haram ne suka yi wa ayarin motocinsu kwanton bauna akan hanyarsu ta dawowa daga Monguno zuwa Maiduguri.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like