Tun a ranar lahadi da maraice ne dai aka ce wadannan mahara suka kai hari garin na Ajari suka hallaka wasu mutane guda shida da kuma wani jami’in soja guda, wanda harma mukaddashin Gwamnan jihar Bornon Alhaji Umar Usman Kadafur ya ziyarci garin na Ajari inda ya jajantawa wadannan mutane.

Barinsa garin ke da wuya da misalin karfe takwas na dare wadannan mahara suka sake kai wani mummunan hari a garin na Ajari inda aka ce sun hallaka mutane guda talatin da ya hada da jami’an soja guda biyar da matasan sa kai da ake kira civilian JTF guda goma sha biyar da kuma wasu fararen hula guda goma.

Garin Ajari dai na da tazarar kilomita hamsin da biyar, daga babban birnin Maiduguri wanda ko watanni biyu da suka gabata sai da Gwamnatin jihar Borno ta mai da wasu ‘yan gudun hijira zuwa garin na Ajari da yanzu haka mazauna wannan garin suka sake ficewa don gudun tsira da ransu.

Bayanai dake cigaba da fitowa daga garin na Ajari yana nuni da cewa, sun kona sansanin sojojin Najeriya, sannan suka yi awon gaba da dukkananin makaman su.

Hakazalika wasu rahotanin na cewa wadannan mayaka sun sake kai hari garin Mungono wanda ya zuwa yanzu dai babu wani takamanman bayani game da wannan harin.

Saurari cikakken rahoton a sauti: