Boko Haram ta kashe mutane 6 a Borno


Mayakan Boko Haram sun kashe mutane biyar tareda yin awon gaba da wasu can daban a wani kazamin hari da suka kai garin Dikwa dake da nisan kilometa 90 da Maiduguri a jihar Borno.

Mutanen da harin ya ritsa da su na daga cikin mutanen da suka shiga dajin wajen neman itacen girki, yan boko Haram sun farmusu sm inda nan take suka kashe mutane biyar a cewar Babakura Kolo wani memba a kungiyar yan sa kai.

Garin Dikwa ya kasance wanin sansani da aka girke yan gudun hijira dubu kusan 70 da matsallar tsaro ya tilastawa baro matsugunin su da kuma ke rayuwa a karkashin kungiyoyin agaji.

A yan watannin nan mayakan kungiyar Boko Haram sun zafafa hare-haren da suke kai wa kan jami’an tsaro da kuma fararen hula.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like