Boko Haram Ta Hallaka Kwamandan Soja Da Sauran Sojoji 20 A Yobe


Wani kwamandan sojin Nijeriya da akalla sojoji 20 sun rasa rayukansu bayan da mayakan Boko Haram suka yi musu kwantan bauna a jihar Yobe.

‘Yan Boko Haram din sun yi wa sojojin kwantar bauna a kan hanyarsu ta dawowa daga Borogozo zuwa Benisheikh.

Wani soja ya bayyana wa TheCable cewa mayakan sun yi wa tawagar sojin kwantan baunar da misalin karfe 6 na yammacin ranar Laraba.

“Suna kan hanyarsu ta zuwa Benisheikh a lokacin da suka fada cikin makiyan. An kashe kwamandan rundunar, wanda kanal ne, da kuma akalla sojoji 20,” sojan ya fada.

Rahotanni sun ce an tura karin sojoji garin kuma an samu tabbacin cewa an kashe kwamnadan rundunar.

A cikin gawarwakin da aka yi rahoton cewa an gano akwai wani kaftin da wasu sojoji hudu.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like