Boko Haram ta aura wa kanta sama da ′yan matan Chibok 20 | Labarai | DWRundunar sojin Najeriya ta gano tsaffin dalibai mata na makarantar sakandaren Chibok ta jihar Borno da ke cikin ‘yan mata 276 da kungiyar Boko Haram ta kwase shekaru takwas da suka gabata. 

A yayin da yake gabatar da matan a Maiduguri, Manjo Janar Christopher Musa, wani babban jami’in sojin Najeriya  ya ce a wurare dabam-dabam sojoji suka yi nasarar samun matan a makon da ya gabata. 

Mary Dauda da sojojin suka gan ta a cikin daji ta ce kawo yanzu Boko Haram ta aura wa mambobinta sama da matan Chibok 20 da ta baro. Ta ce mayakan Boko Haram kan lakada musu duka idan ba su yi sallah ba. Ita kuma Hauwa Joseph ta ce dan Boko Haram din da ya aure ta ya mutu a yayin wani gumurzu da sojojin Najeriya. Ta ce bayan mutuwarsa mambobin kungiyar sun yi watsi da ita da karamin yaron da ta haifa.
Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg