Boko Haram Sun Yi Wa Sojoji Fashin Makudan Kudade


‘Yan Boko Haram sun kwaci makudan kudi da wasu kayyayakin amfani daga hannun dakarun sojin Nijeriya bayan sun kai wa tawagar sojojin hari da safiyar ranar Juma’ar da ta gabata, a tsakanin Azare-Kamuya da misalin karfe 9:00 na safiyar ranar Juma’a, kamar yadda majiyar soji ta sanar da Premium Times.

An yi kazamin musayar wuta tsakanin sojojin da mayakan kungiyar Boko Haram, lamarin da ya yi sanadiyar raunata soja guda daya tare da lalata kayayyakin da sojojin suka dauko da yin awon gaba da wata motar yaki mallakar bataliyar soji ta 231.

Kazalika, mayakan sun yi awon gaba da zunzurutun kudi N15,492,000 da za a biya sojojin dake filin yaki alawus dinsu. Adadin kudin zai isa a biya alawus din dakarun soji 20,000 na tsawon sati guda. Ana bawa kowanne soja alawus din N1,000 kowacce rana.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like