Boko Haram sun kai hari garin Rann inda suka kona asibitin UNICEF


Yan ta’addar kungiyar Boko Haram sun kai hari kan garin Rann dake karamar hukumar Kala Balge ta jihar Borno.

Yan ta’addar sun samu nasarar lalata cibiyar kiwon lafiya daya tilo dake garin wanda ke fuskantar hare-hare daga yan kungiyar akai-akai.

Wata majiya dake garin ta shedawa jaridar The Cable cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile harin bayan da suka dauki tsawon lokaci suna musayar wuta.

Wani mutum mai suna Mijinyawa dake zaune a Kala Balge ,wanda shima ya tabbatar da faruwar harin ya ce yan ta’addar sun isa garin dauke da nau’ikan bindigogi iri-iri kamar na kakkabo jiragen sama da kuma wadanda ake sarrafawa daga kan mota.

“Akwai yiyuwar mutane da dama sun rasa rayukansu a lamarin amma daga labarin da nake samu sojoji sun bawa yan ta’addar kashi,”Mijinyawa ya ce.

“An kuma fadamin cewa wasu yan kauyen dake gujewa harin sun jikkata a musayar wuta.”

A cikin watan Mayun shekarar da muke ciki ne yan kungiyar suka hari garin inda suka kona yi awon gaba da wasu ma’aikatan kiwon lafiya uku.


Like it? Share with your friends!

-1
83 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like