“Boko Haram na kai wa mutane hari amma kuna nan kuna karbar cin hancin ₦1000 a kan kowace mota’ – Zulum ya fadawa sojoji


Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya rufe sojojin dake kula da shingen bincike akan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri da fada a ranar Litinin.

Zulum na kan hanyarsa ne ta zuwa kauyen Jakana inda mayakan Boko Haram suka kai hari a ranar Asabar lokacin da ya ci karo da jerin gwanon ababen hawa a daya daga cikin shingen binciken.

Gwamnan dake nuna alamun an sanar da shi cewa ana karbar kudi daga wurin mutane ya sauka daga motarsa ya kuma wuce kai tsaye inda wasu daga cikin sojojin suke.

“Zan kai karar dukkaninku dake wannan wurin, babu wanda zai yarda da haka. Boko Haram na kai hari kan mutane amma kuna nan kuna karbar ₦1000 akan kowace mota,” ya ce.

Ga fefan bidiyon abin da ya gudana:

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like