Boko Haram na iko da kanana hukumomi 8 a arewacin Borno a cewar wani dan majalisar wakilai


Ahmadu Jaha dan majalisar wakilai ta tarayya daga jihar Borno ya ce yan ta’addar Boko Haram na cigaba da iko da kananan hukumomin 8 cikin goma dake arewacin jihar.

Dan majalisar na jam’iyyar APC na wakiltar kananan hukumomin Damboa/Gwoza/Chibok a majalisar ya bayyana haka ya yin zaman majalisar na ranar Talata.

Jaha wanda ya ke magana kan kudirin dake kira da samar da kudade ga hukumomin tsaro ya ce ana boye wasu batutuwa game da yaki da Boko Haram.

Dan majalisar ya kawo misali da karamar hukumarsa ta Gwoza inda ya ce cikin mazabu 13, uku ko hudu ne kacal da basa karkashin ikon Boko Haram.

A Chibok mazaba biyu ce cikin goma da bata karkashin ikon yan ta’addar hakan abin yake a karamar Damboa inda cikin mazabu 10 daya ce kacal bata karkashin ikonsu.

Bayanin na dan majalisar wakilan zai zowa mutane da da ma mamaki ganin yadda rundunar sojan Najeriya ke cewa babu wani bangare na Najeriya dake hannun Boko Haram.


Like it? Share with your friends!

-1
107 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like