Biyan mafi karancin albashi zai sa a rage ma’aikata -Ngige


Ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Chris Ngige ya ce biyan bukatun kungiyoyin kwadago kan mafi karancin albashi zai sa a kori ma’aikata da dama.

Ya fadi haka ne lokacin da shugabannin kungiyar kwadago ya UTC suka kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa dake Abuja.

Ministan ya ce ana bukatar zunzurutun kudi har naira biliyan 580 domin biyan albashi kamar yadda kungiyar kwadago take bukata.

Ya ce gwamnatin tarayya na kokarin kaucewa yanayin da zai kai sai ta rage wasu daga cikin ma’aikatanta kafin ta iya biyan mafi ƙarancin albashin.

Ngige ya ce tuni aka fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashin ga ma’aikatan dake mataki na 01 zuwa na 06.

Ya roki shugabannin kwadagon da su amince da dan kwarya-kwaryar karin da aka yi kan ma’aikatan dake mataki na 07 zuwa na 17.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like