Shugaban kamfanin BioNTech, Ugur Sahin, ya ba da wannan sanarwa a tattaunawar da ya yi da mujallar nan ta “Der Spiegel” da ke Jamus. Sanarwar ta kara da cewa za su jira hukumar da ke tantance ingancin magunguna a Turai ta ba da amincewarta, binciken da ake ganin zai dauki makwanni hudu zuwa shida.

Yanzu haka dai duka kamfanonin na kokarin ganin an amince da rigakafin nasu da za a iya yi wa kananan yara tun daga wata shida zuwa sama.

Ana ganin saka yaran a jerin masu karbar rigakafin zai taimaka wajen kawo karshen annobar da ma bai wa yaran damar ci gaba da karatunsu kamar yadda ya kamata bayan da suka kwashe tsawon lokaci suna karatu daga gida.