Bindow ya bada umarnin mayar da ma’aikatan kananan hukumomi 80 da aka kora daga aiki


Gwamnan jihar Adamawa, Muhammad Jibrila Bindow ya bayar da umarnin gaggauta mayar da ma’aikatan karamar hukumar Michika su 80 da aka kora daga aiki.

Bindow ya bayar da wannan umarnin ne a wurin taron yakin neman zabensa a karo na biyu da aka gudanar a karamar hukumar Michika.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa a baya wani kwamitin tantance ma’aikata ne ya kore mutanen daga aiki bayan da aka bankado wasu kura-kurai da aka tafka a lokacin da aka dauke su aiki.

Gwamnan lokacin da yake bayar da umarnin ya tuna cewa ya samu goyon bayan mutanen yankin lokacin da yake wakiltarsu a majalisar dattawa.

Shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Ibrahim Bilal ya bayyana cewa gwamnatin Bindow ta kawo sauyi musamman wajen samar da abubuwan more rayuwa.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like