Binciken Masana Ya Nuna Cewa Talauci na rage kaifin kwakwalwar yara


A wani sabon bincike da aka gudanar ya nuna cewa yara wadanda suka fito daga gidaje masu karancin kudin shiga, Inda mahaifan suke da karancin ilimi, zaka samu kwakwalrsu nada rauni tattare da shagaltuwa.

Shugaban masu gudanar da binciken, Farfesa John Spencer, daga jami’ar East Anglia’s da mabiyansa sunyi nazari akan kwakwalwan yaran da suke tsakanin wata hudu da shekaru hudu a kauyukan Indiya.

Sun kwatanta sakamakon da suka samo da yaran da ke gidajen tsakiyar yamma ta kasar America sannan suka gano cewa yaran da suka fita daga gidaje masu karancin kudin shiga, kwakwalwarsu nada rauni tattare da shagaltuwa da abubuwa da yawa.

“Duk shekara, Yara miliyan 250 wa’inda suka fito daga kasashe masu karancin kudin shiga basa kaiwa ga gaci, wannan dalilin ya sa ya kamata a gane illar talauci a kwakwalansu da kuma rayuwarsu gaba daya.”

Spencer ya kara da cewa, Binciken da aka gudanar a baya ya nuna cewa talauci yana da illa sosai akan kwakwalwa, kuma yana haddasa karuwan talauci.
Binciken yayi la’akari da dalilai kamar Ilimin iyaye, kudin shiga, addini, yawan yaran gida da kuma tattalin arziki.


Like it? Share with your friends!

-1
89 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like