Gates, wanda da shi aka kafa kamfanin Microsoft, da matarsa, sun amince za su ci gaba da aiki tare a gidauniya mafi girma a duniya da suka kafa, wacce ake kira Bill & Melinda Gates Foundation.

Cikin wasu sakonnin Twitter iri daya da suka wallafa, sun ce sun amince za su kawo karshen aurensu da suka kwashe shekara 27.

“Mun reni ‘ya’ya uku, mun kuma kafa gidauniya wacce ke aiki a duk fadin duniya da zimmar ganin jama’a sun yi rayuwa cikin koshin lafiya da inganci,” sanarwar ta su ta ce.

“Muna bukatar sirri daga jama’a, a daidai wannan lokaci da iyalinmu ke kokarin fara wata sabuwar rayuwa.”

Sakon Twitter ya kara da cewa, “mun yanke wannan shawara ce, bayan aiki da zurfin tunani da muka yi, mun yanke shawarar mu kawo karshen aurenmu.”