BH sun kona gidaje a kauyen Mifa dake jihar Borno


Mayakan kungiyar Boko Haran sun kona gidaje da dama a Mifa wani kauye dake karamar hukumar Chibok ta jihar Borno.

Wani mazaunin kauyen ya fadawa jaridar The Cable cewa mayakan kungiyar masu yawa sun isa kauyen da misalin karfe 8 na dare inda suka shiga cinnawa gidaje wuta.

“Suna kona gidaje a yanzu da nake magana da kai da yawa daga cikinsu sun zo akan babura inda suka fara kai hari kan kauyen,” a cewar majiyar.

“Bamu san mutanen da abin ya shafa ba, sojoji sun iso yanzu duk da cewa yan ta’addar na cikin kauyukan.”

Ya cigaba da cewa da yawa daga mutanen kauyen sun tsere ya yin da harin ya jefa firgici a Chibok da makotan kananan hukumomi.

Mifa dake da tazarar kilomita 8 daga garin Chibok shine kauye na karshe da ya hada iyaka da dajin Sambisa mai ban tsoro.


Like it? Share with your friends!

-1
66 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like