Kungiyar agaji ta Likitoci na Gari na Kowa da ke kula da ‘yan gudun hijirar a Mujami’u da Jami’o’i, ta nuna fargabar cewar ta yi wu nan da ‘yan kwanaki kalilan ‘yan gudun hijirar su fara mutuwa saboda suna cikin halin rai kwa-kwai mutu kwa-kwai.

Tun daga ranar 23 ga watan Mayun da ya gabata ne dai, fiye da bakin haure 400 wadanda suka kwashe shekaru a kasar, suka fara yajin cin abinci. Sai dai har kawo yanzu, Firaministan Alexander de Croo ya ki yin komai dangane da ka’idojin neman mafaka a kasar.

Yawancin ‘yan gudun hijirar da suka fito daga kasashen kudancin nahiyar Asiya da arewacin Afirka sun rasa ayyukansu ne saboda annobar coronavirus, lamarin da ya haifar musu shiga halin tasku saboda suna zaune ne ba bisa ka’ida ba.