Bayelsa ta bukaci INEC ta sauya ranar gudanar da zaben gwamnan jihar


Gwamnatin jihar Bayelsa ta nemi hukumar zabe ta INEC da ta sauya ranar zaben gwamnan jihar da aka shirya gudanarwa ranar 2 ga watan Nuwambar wannan shekara.

Mataimakin gwamnan jihar,Gboribiogha Jonah,shine ya gabatar da wannan bukatar lokacin da ya jagoranci wata tawagar wakilan gwamnatin jihar zuwa hedkwatar hukumar ta INEC dake Abuja ranar Talata.

Jonah ya ce ya kamata a sauya ranar zaben saboda taci karo da ranar taron addu’ar godiya ga Allah da ake gabatarwa ko wacce shekara a jihar.

Ya yi karin haske kan wahalar da za a fuskanta wajen sauya ranar gudanar da addu’ar wacce a cewarsa doka ce ta samar da ita.

Mahmoud Yakubu shugaban hukumar ta INEC ya ce za su zauna domin duba bukatar da aka gabatar musu.


Like it? Share with your friends!

-1
84 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like