Batun Tikitin Takarar Musulmi Da Musulmi Na Ci Gaba Da Daukan Hankulan Jama’a A Najeriya
ABUJA, NIGERIA – Wasu limaman manyan addinan kasar guda biyu wato Kiristoci da Musulmi sun yi wani taron manema labarai a Abuja, inda suka bayyana mafita.

A daidai lokacin da Jam’iyyar APC mai mulki ke ci gaba da neman wanda za ta tsayar a matsayin mataimakin ‘dan takararsu, mabiya addinai manya guda biyu Muslmi da Kiristoci na kira da babbar murya da a yi takatsantsan wajen nemo wa Bola Ahmed Tinunbu mataimaki.

A lokacin da ya ke bayyana damuwarsa ga manema labarai, Bishop Edward Williams Chanomi, na Majami’ar Prince Chapel International Church da ke Abuja, ya yi tsokaci cewa tun da farko a Najeriya idan an yi shugaba Musulmi to Kirista ne mataimakinsa, saboda haka bai kamata a canza tsarin ba yanzu.

Shi ma tsohon mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara a harkokin addini da aikin hajji, Halliru Abdullahi Maraya, yana ganin tsayar da ‘yan takara mabiya addini daya ya saba wa koyarwar addinin Musulunci.

Llokacin da ya ke tsokaci akan batun tsohon shugaban matasan Kiristoci kuma sakataren Kungiyar Arewa Transformational leaders, Pastor Simon Dolly, ya ce akwai abin dubawa a irin wannan mataki da Jam’iyyu ke kokarin yi a gabanin zaben shekara 2023.

Kungiyoyin addinan biyu sun ce kalubalantar wannan mataki na tsayar da ‘yan takara daga addini iri daya, ya nuna suna kishin ci gaban kasar da al’ummar ta ne baki daya, domin yin haka ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg