Bashir Ahmad ya bayar da gudunmawar Laptop 100 ga wasu makarantu dake Kano


Mai bawa shugaban kasa shawara kan kafafen sadarwar zamani, Mallam Bashir Ahmad ya bayar da gudunmawar na’urar kwamfuta ga wasu makarantu dake karamar hukumarsa ta Gaya a jihar Kano.

Bashir ya bayar da gudunmawar ne ta hannun hukumar habaka fasahar sadarwa ta kasa NITDA.

Shugabannin makarantun da suka amfana da gudunmawar sun ya ba masa kan irin wannan namijin kokarin da ya yi inda suka ce hakan zai bunkasa koyo da koyarwa.

Jumullar na’urar kwamfutar Laptop 100 aka rabawa makarantun.

Wasu yan karamar hukumar sun yabawa, Bashir kan wannan kokarin inda suka ce shine irinsa na farko da wani mai rike da mukamin siyasa ya yi a tarihin karamar hukumar.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like