Barayin shanu sun kashe mutane 8 a Kaduna


Mutane takwas aka rawaito an kashe wasu biyar kuma suka jikkata a wani hari da barayin shanu suka kai kauyen Kurega a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Lamarin ya faru da misalin karfe biyu na ranar Lahadi lokacin barayin shanun suka kai hari kan kauyen.

Kauyen Kurega ya hada iyaka da karamar hukumar Birnin Gwari.

Wadanda suka jikkata an kai su wata cibiyar kula da lafiya a cewar wata majiya dake garin.

Wani mamba na kungiyar bijilante dake garin ya ce mutane 8 barayin shanun suka kashe.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, Aliyu Mukhtar Hussain , ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce mutane uku aka kashe wasu hudu kuma suka jikkata.

“Sun kuma awon gaba da wasu shanu, mun kuma kaddamar kan lamarin ya ce,”ya ce.

Leave your vote


Like it? Share with your friends!

-1
69 shares, -1 points

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg