Barayin Shanu sun kashe mutane 15 a Zamfara


Kwanaki shida bayan an kashe mutane 30 a wani kauye dake Zamfara yan bindiga sun sake kai wani harin kan wani kauyen inda suka kashe mutane 15.

Muhammad Shehu, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN cewa yan bindigar sun kashe mutanen ne a wani kauye da ake kira Zakuna.

Ya ce kauyen na karkashin karamar hukumar Anka dake jihar ta Zamfara.

Shehu ya ce maharan sun dirarwa Zakuna da farkon safiyar ranar Juma’a 1 ga watan Yuni inda suka sace shanu mallakin mazauna kauyen.

A cewarsa Yansakai sune suka gwabza da barayin shanun har ta kai ga sun tsere amma sai suka sake shiri suka dawo inda suka kashe mutane 15.

“Bayan samun rahotan faruwar harin yan sanda sun garzaya kauyen inda suka samu nasarar gano gawarwaki 15 yawancinsu na yan sakai ne,”Shehu ya ce.

Ya kara da cewa an tura karin jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.

Jihar Zamfara ta dade tana fuskantar hare-hare daga wasu da ake zaton barayin shanu ne da kuma yan fashi da makami.

Leave your vote


Like it? Share with your friends!

-11
74 shares, -11 points

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg