Barayi sun kona ofishin yansanda a Kaduna inda suka kashe jami’ai biyu


Wasu da ake kyautata zaton barayi ne sun kona wani caji ofis na ƴansanda dake kauyen Kakangi a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna inda suka kashe ƴansanda biyu nan take.

Jaridar The Cable ta gano cewa lamarin yafaru ne da misalin karfe biyar na asuba bayan da maharan suka shigo akan babura inda suka fara harbin ke me uwa da wabi.

Wani mazaunin kauyen wanda bai so a bayyana sunansa ya ce mutanen da ake zargi barayin ne dake dauke bindigogin sanfurin AK-47 sun kuma kashe wasu mutane biyu daban.

An kai wadanda suka jikkata a harin ya zuwa asibiti domin samun kulawa.

Kauyuka dama garin na Birnin Gwari sun dade suna fuskantar hare-hare daga barayi da kuma masu garkuwa da mutane.


Like it? Share with your friends!

-1
90 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like