Barayi sun kashe mutane 10 a Birnin Gwari sa’o’i 72 bayan da aka kafa sansanin soja a garin


Yan bindiga dauke da makamai sun kashe a kalla mutane 10 a wasu kauyuka dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Barayin sun kai harin ne a ranar Talata da misalin karfe 5:00 na yamma inda suka shiga harbi tare da kona gidaje.

Lamarin na faruwa ne kasa da kwanaki uku bayan da babban hafsan sojan kasarnan, Tukur Buratai, ya bawa sojoji wa’adin makonni uku na su fatattaki yan fashi da kuma barayin da suka addabi yankin.

Buratai ya bayyana haka lokacin da yake kaddamar da sansanin soja a garin.

A wata sanarwa da ta fitar kungiyar Birnin Gwari Vanguard mai fafutukar samar da tsaro da kuma kyakkyawan shugabanci ta ce mutanen da abin ya shafa suna matukar bukatar taimako.

An ce yan bindigar sun dauki tsawon sa’a uku suna cin karensu babu babbaka ya yin kai harin.

“Barayin sun kona gidaje da kuma rumbunan kayan abinci a kauyukan da abin ya shafa,”a cewar sanarwar.

“Kauyukan da abin ya shafa na bukatar taimakon abinci, matsuguni da kuma kayan sawa.”


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like