Barayi na iko da wasu yankuna a jihar Katsina- Masari


Barayi da kuma masu garkuwa da mutane sun kwace iko da wasu yankuna na jihar Katsina.

Gwamnan jihar,Aminu Bello Masari shine ya fadawa mukaddashin babban sifetan ƴansanda na kasa, Muhammad Adamu.

“Wadannan barayi suna kai hari a lokutan da suka ga dama, suna illata mutane idan sun ga dama tare da lalata rayuka da dukiya a lokutan da suka ga dama,”Masari ya fadawa babban sifetan haka ta bakin mataimakinsa Mannir Yakubu.

“A wasu wuraren muna fama da masu garkuwa da mutane wadanda ba wai ka wai akan tituna suke sace mutane ba, a’a har cikin gidajensu suke binsu,”inda har ya yi misali da surukar gwamnan jihar da aka sace ta tana cikin gidanta.

Tunda fari babban sifetan ya ce yazo jihar ne domin duba kalubalen tsaro da jihar take fama da shi musamman ayyukan barayi da kuma masu garkuwa da mutane.


Like it? Share with your friends!

-1
74 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like