‘Barayi dauke da makamai sun kashe mutane 17 a kauyukan Zamfara


Barayi dake dauke da makamai sun kashe akalla mutane 17 a wasu kauyuka uku dake karamar hukumar Birnin Magaji ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan dake kan babura sun kai farmaki kauyen Gidan Kaso ranar Asabar inda suka kashe mutane 7.

“Sun ki yarda su bari mazauna kauyen su dauki gawar mamatan domin a yi musu jana’iza har sai da jami’an tsaro da kuma yan bijilante su ka hadi suka shiga kauyen,” a cewar Sani Tukur dake zaune a kauyen.

Wasu ƙarin rahotanni sun bayyana cewa barayin dake dauke da makamai sun kai farmaki kauyen Dan Dambo inda suka kashe mutane hudu tare da yin awon gaba da dabbobi masu yawa.

Mutane bakwai daga kauyen Kokoya dake makotaka aka kashe lokacin da suka kawowa mutanen Dan Dambo dauki sa’ilin da ake fafatawa da maharan.

Har ya zuwa yanzu rundunar yansandan jihar Zamfara ba tace komai ba game da faruwar harin.


Like it? Share with your friends!

-2
83 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like