Ban ce Buhari ya sauka daga mulki ba- Babangida


Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi watsi da labaran da ake yadawa ta kafar Intanet dake cewa ya shawarci shugaban kasa Muhammad Buhari ya sauka daga kan mulki.

Babangida a wata sanarwa da ofishinsa na yada labarai ya fitar ta bayyana cewa tsohon shugaban kasar bai mallaki wani shafi ba na kafafen sadarwar zamani ballantana ya yi amfani da kafar wajen bayyana ra’ayinsa kan abinda ke faruwa a ƙasarnan.

Sanarwar ta ce an jawo hankalin tsohon shugaban kasar kan wani shafi na kafar sadarwar Twitter da kuma sauran kafafen sadarwar zamani mai dauke da suna tsohon shugaban kasar.

Ta kuma shawarci jama’a musamman masu amfani da kafar sadarwar zamani ta Twitter cewa tsohon shugaban bashi da shafi a kafar ko kuma kowace kafar sadarwar zamani.


Like it? Share with your friends!

-2
74 shares, -2 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like