Ban aikata laifin da ake zargi na da aikata wa ba – Maryam Sanda


Matan nan Maryam Sanda da ake zargi da kashe mijinta, Bilyaminu Bello a bara ta bayyana a gaban babban kotun babban birnin tarayya Abuja a ci gaba da sauraron shari’ar, ta bayyana wa kotun cewa ita ba ta aikata laifin da ake zarginta da aikatawa ba.

Ana kuma zargin mahaifiyar Maryam Sanda, ‘Hajiya Maimuna Aliyu’, kaninta, ‘Aliyu Sanda’ da kuma ‘yan aikin gidanta ‘Sadiya Aminu’ da taimaka wa Maryam gurin goge jinin marigayi Bilyaminu Bello bayan ta kashe shi. Amma duka sun ki amincewa da sun aikata laifin.

A zaman kotun na jiya Talata, Lauyan wadda ake kara, Olusegun Jolaawo ya fada wa kotun cewa shaidun da bangaren masu kara su ka gabatar ba su gamsar da har za a bar wanda ake zargi ta kare kanta ba, dan haka ya roki kotun da ta wanke wadda ya ke karewa daga zargin aikata laifin kisan kai.

Lauyan mutum ukun da aka zargesu da taimaka wa Maryam Sanda, Hussain Musa, shi ma ya nemi kotun da ta sallami wadan da ya ke karewa tare da wankesu daga zargin da ake yi musu domin a cewarsa har yanzu bangaren masu kara sun kasa kawo kwakwaran hujja da zai sa a kyaleau su kare kansu.

Shi ma a nashi bangaren, Lauyan bangaren da ke kara Fidelis Ogbobe y kalubalanci bukatar Lauyan wanda ke kare a wacce ake kara, inda ya bayyana cewa, sun gabatar da shaidu da zai gamsar da kotun har ta bar wadda ake zargi ta kare kanta.

Har ila yau ya kara da cewa, akwai shaidu da hujjoji da suka danganta wadan da ake kara da aikata wannan laifi. Dan haka ya ce ya ya na neman kotu da ta amince ta bai wa wadan da ake zargi su kare kansu daga zargin da ake yi masu.

Yanzu dai alkalin kotun, Mai shari’a Yusuf Halilu ya sanya ranar 4 ga watan Afirilu a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraron kararar tare da duban yiwuwar ko kotun za ta bai wa wadan da ake zargi su kare kansu.


Like it? Share with your friends!

-3

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like