Bafarawa Zai Duba Yiwuwar Tsayawa Takarar Shugaban Kasa a Zaben 2019


Akwai yiyuwar tsohon gwamna jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, Garkuwan Sokoto zai amince da kiraye kiraye da ake yi masa dangane da fitowa cikin masu son tsayawa takarar shugabancin Nijeriya a shekarar 2019 karkashin jam’iyyar PDP nan gaba a cikin watan Mayu mai zuwa.

Bayanin tabbacin cewar Bafarawa zai amsa kiran na daga cikin wani bincike da aka yi a sakamakon wata tattaunawa da akeyi yanzu haka da wasu kungiyoyin yekuwar tallata tsohon gwamna Bafarawa da shugabanin jam’iyyar PDP na jihohin Kebbi, Katsina, Gombe da Minna a makon nan da ya gabata inda wasu matasa daga kawancen kungiyoyin ci gaban jam’iyyar PDP na Arewa suka hadu don fito da hanyoyin baiwa tsohon Gwamna Bafarawa goyon baya da shawara na ya fito takarar mukami bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aiyana bukatar da yake da ita na neman kujerar shugabancin Nijeriya a karo na biyu.

Attahiru Bafarawa wanda ya taba neman wannan kujerar a shekarar 2007 karkashin jam’iyyar DPP yazo kuma na 4 a jerin yawan kuri’a da karbuwa a Nijeriya ya so ya sake gwada kwarjininsa karkashin jam’iyyar ACN amma saboda wani dalili ya janyewa Nuhu Ribadu a shekarar 2011.

Baya ga kasancewa daya daga cikin gwamnoni Nijeriya daga Arewa da suka yi fice a shekarar 1999 zuwa 2007 dangane da kare muradun Arewa da yan Arewa; Bafarawa ya kasance daya daga cikin muhimman yan siyasa 10 a Nijeriya da suke da karbuwa, fice da muhimmanci, mussaman na kokarin ganin ya kwato ma Arewa hakkokinta a lokuta dabam dabam.

Bafarawa wanda tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ne suka fara zancen hadin kai da hadakar jam’iyyu zuwa daya don fuskantar gwamnatin PDP a lokacin, shine ya dauki nauyi rubuta da buga tsarin mulkin da yanzu haka jam’iyyar APC take amfani dashi, kuma yana daya daga cikin muhimman mutanen da suka kirkiro da jam’iyyar APC har ta samu rajista kamin ya barta ya koma PDP saboda sabanin ra’ayi da wasu yan siyasa a jiharsa.

Idan har dai tsohon gwamna Bafarawa ya aiyana amincewa da neman kujerar a cikin jam’iyyar ta PDP, hakan zai sanya cewar, a Arewa PDP tana da yan takara har guda shida kenan da suka nuna alamu ko tabbatar da zasu nemi goyon baya a yanzu.

Sauran sune Alhaji Atiku Abubakar, Alhaji Sule Lamido, Sanata Ahmed Makarfi, Alhaji Ibrahim Shekarau da Gwamna jahar Gombe, Alhaji Ibrahim Dankwambo.

A makon jiya a garin Katsina, Bafarawa ya shaidawa ‘yan jam’iyyarsa ta PDP cewar, akwai bukatar dukkan wadanda suka yiwa yan kasa laifi, mussaman a PDP dasu nemi gafara, su tuba ga al’umma bisa gaskiya don kuwa PDP ta tabka kura-kuran da ala dole sai anyi tuba na gaskiya, kamin a koma amincewa da ita.

Haka ma a wata hirarsa da gidan telebijin na Liberty Kaduna, Tsohon gwamna Bafarawa ya baiyana mafi rinjayen yan siyasa a Nijeriya da suka shude da masu rike da iko a yanzu cewar suna da laifi dangane da amfani da addini ko kabilanci wajen neman biyan bukatunsu da rarraba hankulan al’umma ga samu biyan bukata wadda a karshe zasu yi watsi da jama’a.

Bafarawa ya baiyana cewar, kusan shugabani da suka mulkin Nijeriya zuwa yau suna da laifuka iri iri, amma muddin aka tuba za a samu faida da ci gaban kasa.

Kokarin samun shugaban jam’iyyar PDP na jihar Sokoto, Alhaji Ibrahim Milgoma don tabbatar da gaskiya bayanin tsayawa takarar Attahiru Bafarawa yaci tura, amma wani na kusa dashi ya baiyana cewar akwai kamshin gaskiya ga labarin, don kuwa yanzu haka Bafarawa yana a kasa mai tsarki wurin aikin Umrah, kuma idan ya dawo zai yi taro na mussaman da yan jam’iyyarsa a yankin Arewa dangane da baiyana musu matakin da ya dauka.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like