Babu Abinda Zai Hana Ni Magana Kan Mawuyancin Halin Da Ake Ciki A Kasar Nan – Aisha Buhari


Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana cewa, babu abinda zai hana ta magana a kan kalubalen da kasar nan ke fuskanta.

Ta bayyana cewa, ‘yancin magana hakki ne na kowanne dan kasa kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya tanada.

Ta ce babu gudu ba ja da baya, tana bayan dokar da majalisar tarayyar kasar nan ke yunkurin kafawa a kan daidaita soshiyal midiya.

Uwargidan shugaban kasan ta tabbatar da cewa ba za a iya hanata magana ba.

Ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis 5 ga watan Disamba a birnin Landan.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like