Babbar mota ta nike mutane biyu a Benue


Da safiyar ranar Talata ne wata motar tirela markade wasu mutane biyu har lahira akan sabon titin Otukpo dake Makurdi babban birnin jihar Benue.

Kwamandan hukumar kiyaye hadura ta tarayya FRSC a jihar Benue, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da ya yi da wakilin jaridar Daily Trust ta wayar tarho ya ce wadanda abin ya rutsa da su sun hada da wani dan acaba da kuma fasinja mace da ya dauko.

Baba ya ce hatsarin ya faru ne da misalin karfe 08 :40 na safe.

Ya kara da cewa motar ta nike mutanen ta yadda baza a iya gane kamanninsu ba.

Shugaban na hukumar ta FRSC ya ce sunan dake jikin katin ATM din matar ne ya sa aka gane ta.

Tuni dai direban motar ya kai kasa ofishin yan sanda na B dake Makurdi.


Like it? Share with your friends!

-1
57 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like