Babbar Malamar Addinin Musulunci A’isha Lemu Ta Rasu


A yau, Asabar, 5 ga watan Junairu, 2019, Allah ya yi wa babbar malamar addinin Musuluncin nan ‘yar asalin kasar Birtaniya, Bridget Aisha Lemu, rasuwa. Malamar ta rasu tana da shekaru 78 a duniya.

Malama Bridget A’isha Lemu, wadda ta kasance fitacciyar marubuciyar littafan addinin Musulunci, baturiyar kasar Birtaniya ce wadda ta karbi addinin Musulunci a shekarar 1961.

An haife ta a garin Poole na kasar Ingila a shekarar 1940. A’isha ta soma wasuwasi a kan addininta na farko tun tana shekaru 13. Hakan ne ya sa ta soma bincike a kan wasu addinai kamar addinin Hindu da kuma Buddha na kasar Chana. Ta yi karatu a jami’ar birnin Landan karkashin makarantar nazarin mutanen gabashin Asia da Afirka, ‘School of Oriental and African Studies (SOAS)’, inda ta maida hankali a bangaren tarihi, yare da kuma al’adun kasar Chana. A lokacin da take can ne ta hadu da wasu Musulmai da suka damka mata adabin addinin Musulunci domin ta karanta. Hakan ya sa ta karbi addinin Musulunci a cibiyar addinin Musulunci a shekarar 1961.

Musuluntarta ke da wuya ta taimaka gurin kafa kungiyar mabiya addinin Musulunci a jami’ar, inda ta zamo sakatariyar kungiyar ta farko. Bayan nan kuma ta taimaka gurin kafa tarayyar kungiyoyin dalibai mabiya addinin Musulunci.

Bayan kammala karatu a SOAS, Aisha Lemu ta koma digiri na biyu a bangaren koyar da yaren Turanci a matsayin yaren kasar waje. A lokacin da take karatun ne Allah ya hada ta da mijinta, Sheik Ahmad Lemu, wanda shima yake karatu a wata kwalejin jami’ar Landan, sannan kuma shima yake ayyukan yada addinin Musulunci a kwalejin.

Bayan ta samu kwalin digirinta na biyu a fannin koyarwa sai ta taho jihar Kano ta kasar Nijeriya a watan Agusta 1966 domin ta yi aikin koyarwa a makarantar koyon yaren Larabci, inda Sheik Ahmad Lemu yake a matsayin shugaban makarantar. Sun yi aure a watan Afrilu, 1968, inda A’isha ta zamo matarsa ta biyu. Bayan nan A’isha ta koma Sakkwato inda ta zamo shugabar makarantar ‘yan mata ta gwamnati.

A shekarar 1976 Sheik Ahmad Lemu ya zamo shugaban alkalan kotun daukaka kara ta addinin Musulunci a jihar Neja, yayin da Aisha take shugabar kwalejin mata da ke Minna. Ma’auratan sun kafa gidauniyar ilimin addinin Musulunci “Islamic Education Trust (IET)” wadda take da rassa a jihohin Nijeriya da dama. IET na da ofisoshi da dakunan karatu da cibiyoyin karatun manyan mata. A’isha ta kasance mamba na kwamitin ilimin addinin Musulunci, wanda hukumar bincike da bunkasa ilimi ta Nijeriya ta kafa domin yin bitar manhajar darasin ilimin addinin Musulunci na makaratu.

A shekarar 1985, A’isha ta samar da tarayyar kungiyoyin mata Musulmai (FOMWAN) inda aka zabe ta a matsayin Amirar kungiyar ta farko. Ta shafe shekaru hudu cur tana shugabantar kungiyar.

Wasu daga cikin ayyukan da ta wallafa sun hada da:

– A student’s introduction to Islam. Macmillan Education, London 1971.
– Gabatar da addinin Musulunci ga dalibi.
– Northern Nigerian Pub. Co., Zaria 1976.
– Islamic citizenship and moral responsibility. Islamic Education Trust, Minna 1979.
– Students’ Islamic Society Branch Organization (Islamic Education Trust Guidelines series). Islamic Education Trust, Minna 1979.
– Methodology of primary Islamic studies. A handbook for teachers. Islamic Publications Bureau, Lagos 1980.

– A critical look at the theory of evolution (=IIFSO 46). International Islamic Federation of Student Organizations, Salimiah [Kuwait] 1982.
– A degree above them. Observations on the condition of the northern Nigerian Muslim woman. Islamic Education Trust, Minna and Gaskia Corporation respectively, Zaria 1983.
– The theory of evolution from the Islamic perspective (=International Islamic Federation of Student Organizations, p. 46). Translated by Ayisha Niazi. IIFSO, Salimiah (Kuwait) 1983.
– Tawhid and fiqh. Belief and jurisprudence (= Junior Islamic studies. Book 1). Islamic Education Trust, Minna.
– Lessons on the Qur’an (=Junior Islamic studies, Book 2A). Hudahuda, Zaria and Hodder & Stoughton, London 1986. ISBN 0-340-32791-X.
– Junior Qur’anic Arabic (=Junior Islamic studies . Book 2B). Hudahuda in association with Hodder and Stoughton, Sevenoaks, and Zaria, 1986. ISBN 0-340-32790-1.
– Tahdhib (moral education) and Sirah (=Junior Islamic studies . Book 3). Islamic Education Trust, Minna.
– The Ideal Muslim Husband . Islamic Education Trust (Publications Division) Minna 1987. Reissue at Al-Saadawi Publications, 1992. ISBN 1-881963-03-9
resp. ISBN 978-1-881963-03-5 .
– Islam, the religion of the future. The Islamic Union of Hong Kong, Hong Kong 1988.
– Islamization of Education. A Primary LevelExperiment in Nigeria. In: Muslim Education Quarterly, volume 5 No. 2, 1988.
– The role of Muslim women in the 15th century Hijrah. In: Ramatu Abdullahi, Muslim Sisters Organization of Nigeria (eds.): The Muslim woman. Challenges of the 15th Hijra . Woye & Sons, Ilorin and Islamic Publications, Lagos 1988. *** ”
– Gari ya waye (Nazari a kan matsayin mata Musulmi a Arewacin Najeriya). Translated by Shuayb Haruna Gambo Langen. Mosque Foundation, Kaduna 1989.
– Islamic studies for senior secondary schools. Book 1. Islamic Publications Bureau, Lagos 1989. ISBN 978-2470-27-9 .
– Islamic studies for senior secondary schools . Book 2. IET, Minna 1990.
– Muslim women and marriage under the Shariah rights and problems faced. In Awa U Kalu and Yemi Osin Bajo (ed.): Women and children under Nigerian law (=Federal Ministry of Justice, Law Review series Vol. 6.). Federal Ministry of Justice, Lagos, 1990. ISBN 978-2439-06-1.

– Laxity, moderation, and extremism in Islam. Islamic Education Trust, Minna,
1991. ISBN 978-30722-2-6.
– The Ideal Muslim Wife. Islamic Education Trust (Publications Division), Minna 1992. ISBN 978-2159-06-9.
– Animals in Islam. Spectrum Books, Ibadan and Islamic Education Trust, Minna 1993. ISBN 978-2462-33-0.
– Laxisme, modération et extrémisme en Islam (= Occasional papers. 5). Translation of Michèle Messaoudi.

International Institute of Islamic Thought, Herndon, Virginia, and London, 1995. ISBN 0-912463-96-1.
– Islam and Alcohol. Edited version of a lecture delivered at Advanced Teachers’ College Minna on the occasion of Id-al-Maulud, February 1981. Al-Saadawi Publications, Alexandria (Virginia) 1996. ISBN 1-881963-02-0.

– Islamic ‘aqidah and fiqh. A textbook of Islamic beliefs and jurisprudence . IQRA’ International Educational Foundation, Chicago 1996. ISBN 1-56316-061-7. Sikap ekstrem. Penyakit dakwah Islam. International Institute of Islamic Thought, Petaling Jaya 1996.
– Islamic tahdhib and akhlaq. Theory and practice. IQRA’ International Educational Foundation, Chicago, 1997. ISBN 1-56316-320-9.

– A holistic approach to teaching Islam to children. A paper presented at the Conference on Private Islamic Schools, 12–13 August 1994, held in Minna by the Islamic Education Trust on behalf of the Nigerian Da’wah Coordination Council (NDCC). IET Publications Division, Islamic Education Trust, Minna, 2001. ISBN 978-2159-45-X.

– Child upbringing and moral teaching in Islam. A paper presented at Abuja Muslim Forum Seminar on Child Upbringing, a Divine Obligation, a Complementary Responsibility, December 1977 . Islamic Education Trust, Minna, 2001. ISBN 978-2159-44-1.

– Teaching for tolerance in Nigeria . In: Recep Kaymakcan, Oddbjørn Leirvik, Oslo Coalition on Freedom of Religion or Belief (eds.): Teaching for tolerance in Muslim majority societies . Center for Values Education (DEM) Press, Istanbul, 2007. ISBN 978-975-6324-98-1

Allah ya ji kan Malama Aisha Lemu


Like it? Share with your friends!

3
69 shares, 3 points

Comments 2

Your email address will not be published.

  1. Allahu akbar kabeeraa!!! Allah ya jiqanta, gaskiya tayi wa Musulunci da Musulmai hidima ba dan kadan ba. Allahumma alhiqha bin-nabiy Muhammad s.a.w

You may also like