Ba’a saka dokar hana fita a Kano ba- Hukumar ‘Yansanda


Kwamishinan ‘yansandan jihar Kano ta hannun me magana da yawun ‘yansandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ta karyata rade-radin dake yawo a shafukan sada zumunta cewa wai an saka dokar hana fita a jihar.

DSP Abdullahi Haruna ya gayawa kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN cewa wannan labarin na saka dokar hana fita dake yawo a shafukan sada zumunta karyane, kawai wasu ne dake son kawo tashin tashina suka kirkire shi.

Ya kara da cewa, idan akwai maganar saka dokar tabaci jama’a zasu ji ta kafofin watsa labarai ingantattu.


Like it? Share with your friends!

-2

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like