Ba Zan Sake Yin Soyayya Da ‘Yan Matan Nijeriya Ba, Cewar Suleman Saurayin Baturiya


Matashi Suleman Isa Panshekara wanda masoyiyarsa Batuturiya mai suna Janine Sanchez ta biyo shi zuwa Kano daga kasar Amurka, ya bayyana cewa a yanzu ba zai iya yin soyayya da wata ‘yar Nijeriya ba.

A hirar da BBC Hausa ta yi da shi, Suleman ya bayyana cewa “gaskiya matanmu ba su iya soyayya ba, ko dai za ka ga suna da wata bukata ko kuma suna da buri amma idan baturiya ta ce tana sonka, toh tana fadin haka ne daga zuciyarta.”

Masoyan dai sun fara haduwa ne ta shafin Instagram a shekarar da ta gabata inda ta kai su ga fara soyayya da junansu, gashi yanzu har ana maganar aure.

Isa ya ce iyayensa sun amince ya auri masoyiyar tasa Janine kuma nan da watan Maris za a yi bikinsu inda za su wuce Amurka. A baya Legit.ng ta rahoto cewa cibiyar tabbatar da shari’ar Musulunci ta jihar Kano, Hisbah, a ranar Asabar ta gayyaci dattijuwar Ba Amurkiyar da ta garzayo Kano don auren masoyinta, Sulaiman Isa, zuwa ofishinsu don amsa tambayoyi.

Dattijuwar mai shekaru 45 kuma mahaifiyar ‘ya’ya biyu, Jeanine Delsky, ta isa Panshekara ne don haduwa da saurayinta Sulaiman wanda suka hadu a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.


Like it? Share with your friends!

0

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like