CP Hussaini Rabiu ya bayyana hakan ne a yayin kai ziyara ga wasu daga cikin jami’an yan sanda da suka ji rauni a wani harin yan bindiga da ya yi sanadiyar mutuwar wasu jami’an tsaro 13.

Haka kuma, CP Hussaini Rabiu ya ce rundunar ta kuduri aniyar ci gaba da gudanar da ayyukanta na yaki da ‘yan bindiga masu tayar da kayar baya da sauran masu aikata muggan laifuka a cikin jihar Zamfara.

To sai dai ya yi kira ga dukkan ‘yan kasa masu bin doka da oda, da su hada kai da jami’an tsaro don samun nasarar kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta baki daya.

Rahotanni dai sun yi nuni da cewa, wasu yan bindiga sun kai harin kwanton bauna ga jami’an ‘yan sandan da ke kan hanyar su ta zuwa kai dauki ga wasu al’umma da ke kusa da kauyen Kurar Mota a cikin karamar hukumar mulkin Bungudu, inda suka hallaka jami’ai 13 kamar yadda wakilinmu a jihar ya shaida mana.

Yan sandan sun gamu da ajalinsu ne a daidai lokacinda su ke kan hanyarsu ta kaiwa al’umma dauki bayan samun kiran gaggawa na neman agaji.

A yayin tabbatar da afkuwar lamarin a ranar lahadi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya ce jami’ansu sun yi musayar wuta da ‘yan bindigar ne don dakile yunkurin shiga wasu kauyukan da su ka nufa.

Haka kuma, SP Shehu ya bayyana cewa, a nasu bangaren ma ’yan bindigan sun rasa mambobinsu a musayae wutar.

Ya kuma bayyana cewa rundunar ‘yan sandan ta kaddamar da aikin farautar’ yan bindigar da suka yi wa jami’an rundunar kwanton bauna a kauyen Kurar Mota.

An dade ana samun irin wannan harin na kwanton-bauna kan jami’an tsaro a lokuta da dama da su ke kan aikin sauke nauyin da ya rataya a wuyan su na tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.