Ba Na Tsoron Karawa Da Kwankwaso – Shekarau


Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ba ya tsoron karawa da dan takar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Alhaji Sani Madakin Gini, a zaben da za a kada ranar Asabar na kujerar sanatan Kano ta tsakiya.

Da yake magana da manema labarai a jiya, Malam Shekarau ya ce ya so a ce da Kwankwason ma zai fafata ba wani yaronsa ba.

Malamin ya kuma yi ikirarin cewa Sanata Kwankwaso bai taba tako kafarsa mazabarsa ba a tsawon shekaru uku da rabi balle har ya gana da mutanen mazabar.

Tsohon ministan ilimin ya kuma ce babu wani sabani a tsakaninsa da Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar yadda wasu suke ta yayatawa.


Like it? Share with your friends!

1
87 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like