Ba Da Sanin Gwamnati Jami’an Tsaro Suka Yi Wa Zauren Majalisar Dattawa Kawanya Ba – Osinbajo


Osinbajo ya ce aikin wanda suka aiwatar ba tare da sanin gwamnati ba abin Allah-wadai ne kuma ba wanda gwamnati za ta kau da kai daga shi ba ne.

Shugaban ‘kasar na riko, Yemi Osinbajo, ya bayyana ‘kawanyar da jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka yi a matsayin saɓa wa dokar kundin tsarin mulkin ‘kasa.

Ya bayyana ɓacin ransa a kan jami’an tsaron farin kayan (DSS) a cikin wani jawabi da mai magana da yawunsa, Laolu Akande, ya sanya wa hannu, inda ya bayyana cewa “an aikata aikin wanda ya saɓa doka ba tare da sanin gwamnati ba.”

Jawabin yake cewa: “Shugan ‘kasa na riko, Yemi Osibanjo, SAN, ya bayyana kwace ikon zauren majalisar dokoki wanda ba bisa izini ba a safiyar yau a matsayin saɓa wa dokar kundin tsarin mulkin ‘kasa, doka ta shari’a da kuma dukkan wasu karɓaɓɓun ra’ayoyin doka da oda.

“Dangane da jawabinsa, dukkan wani aikin da ya saɓa wa doka wanda aka aikata ba tare da sanin gwamnati ba abin Allah-wadai ne sannan abu ne da gwamnati ba za a kauda kai daga shi ba.

“Saboda haka, Farfesa Osinbajo yana tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewar za a za’kulo dukkan jami’an da ke da hannu a cikin wannan mummunan aikin sannan zasu fuskanci ladabtarwa.”

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like