Ayyukan Hanyoyin Da Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Yi Karkashin Jogarancin Gwamna El-Rufai


Gwamnatin Jihar Kaduna a shekaru uku da rabin da ta yi a karagar mulki, ta yi sababbin hanyoyi kuma ta gyara tsofaffin hanyoyi guda 130 a fadin jihar.
• An yi hanyoyin cikin gari na tsawon kilomita 140. Wasu an kammala, wasu kuma na matakai daban daban na kammalawa.
• An yi manyan hanyoyi da ake kira ‘Intercity roads’ 16 na tsawon kilomita 414.8. Su ma an kammala wasu, wasu kuma suna matakai daban daban na kammalawa.
• An yi hanyoyin karkara guda 17 na tsawon kilomita 172. Su ma an kammala wasu, wasu kuma suna matakai daban daban na kammalawa.
Wasu fitattun hanyoyin da aka yi ko ake kan yi sun hada da:
➢ Fadada babban tagwayen titin Ali Aliku zuwa ‘yan uku, wanda ta tashi daga Gadar Kawo zuwa Shataletalen Lugard Hall.
➢ An Tagwayentar da titin shiga Rigasa, wanda aka fi sani da ‘Zaria Road’ wanda ta kama daga Bakin Ruwa zuwa tashan jiirgin kasa da ke Rigasa, Kaduna.
➢ Ana tagwayentar hanyar Unguwar Dosa, wanda ake kira ‘College Road’ zuwa ‘Sabon Birni Road’.
➢ An tagwayentar da hanyar kawo, Kaduna.
➢ Tagwayentar da hanyar PZ zuwa Dogarawa a karamar Hukumar Sabon Gari.
➢ An tagwayentar da titin PZ zuwa Dogarawa, a Karamar Hukumar Sabon Gari.
➢ An tagwayentar da hanyar Sabon Birni da ke Kawo a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa
➢ An tagwayentar da hanyar
➢ An yi sabon titi da ake kira ‘Link Road’ a Rigasa, wanda ya hade tashar jirgin kasa da titin Mando.
➢ An yi hanyoyin cikin gari a cikin garin Ikara
➢ An yi hanyar Hanwa da ke GRA a Karamar Hukumar Sabon Gari
➢ Ana aikin hanyoyin cikin gari a Zuntu da ke Karamar Hukumar Makarfi
➢ Ana aikin hanyar Bagoma – Randagi – Kakangi da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari
➢ Ana aikin hanyar Kutemeshi – Kuyello da ke Karamar Hukumar Birnin Gwari
➢ Ana aikin hanyar Bomo – Kwakwaren Manu da ke Karamar Hukumar Sabon Gari da Giwa.
➢ Ana aikin honyoyin cikin gari a Karamar Hukumar Sanga
➢ Ana aikin hanyar da ta tashi daga Kofar Gidan Bellon Gima zuwa Kofar Galadima a Karamar Hukumar Zariya.
➢ An fara aikin hanyar da ta tashi daga Kofan Doka zuwa Kofar Galadima inda aka biyya na gidajen da aka rushe na kimanin kudi Naira miliyan 400.
➢ An ci gaba da aikin hanyar da ta tashi daga Tukur Tukur Zariya zuwa GRA Sabon Gari
➢ An yi hanyoyin cikin gari na kilomita 10 a garin Manchok da ke Karamar Hukumar Kaura
➢ An kammala hanyar cikin garin Kagoma da ke Karamar Hukumar Jema’a na tsawon kilomita 10.
➢ An tagwayentar da hanyar Sabon Birni da Kudan, a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa wadda tsawonta ya kai kilomita 2.6
➢ Ana aikin hanyar Dutsen Wai zuwa Ancha
➢ Ana aikin hanyoyi a cikin garin Anchau da Dutsen Wai na tsawon kilomita 10.
➢ An fara aikin hanyoyin cikin unguwa (township roads) a Rigasa guda 20 na tsawon kilomita 20
➢ An yi hanyoyi guda 75 a Unguwar Barnawa, Kaduna.
➢ Ana aikin hanyoyi cikin unguwanni a kabala.
➢ An yi aikin hanyoyi 7 a unguwan Sarki na tsawon kilomita 2.7
➢ An fara aikin hanyoyi 26 a Unguwan Rimi na tsawon kilomita 6.7
➢ An fara aikin hanyoyi 9 a cikin Unguwan Malali, Kaduna.
➢ An fara aikin hanyoyi 44 a Kabala na tsawon kilomita 13.5.
➢ An yi hanyoyi Wari da Benin streets a Karamar Hukumar Sabon Gari, Zariya.
➢ An fara aikin hanyar Kwanar Rimi zuwa Kofar Yamma, karamar Hukumar Kudan.
➢ An fara aikin hanyar Tashar Zaki zuwa PHC, a Karamar Hukumar Kudan.
➢ An fara aikin hanyar Hunkuyi Academya zuwa Eastern Bye Pass, a Karamar Hukumar Kudan.
➢ An fara aikin hanyar Hunkuyi Eastern Bye Pass
➢ Ana aikin hanyar Fadan kamanta- Yangal- Walijo(22.5km) a karamar hukumar Zangon Kataf
➢ An fara aikin hanyar cikin unguwanni a Hayin Banki(6.9km)
➢ An fara aikin hanyar 96 a Gundumar Doka a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa
➢ An gyara tagawayen hanya ta Nnamdi Azikiwe, Kaduna.
➢ Ana aikin hanyoyi a cikin Unguwar Abakpa da ke garin Kaduna
➢ Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu suna gina gidaje gidaje masu sauki( affordable mass housing). Su ma wannan aikin ya yi nisa. Sannan kuma wasu kamfanoni guda 14 suna nan suna aikin gina cibiyoyin hada-hada (neighbourhood centers) da kuma wasu kamfanoni 16 suna aikin gina kasuwannin zamani a garin Kaduna, Zariya da Kafanchan.


Like it? Share with your friends!

1
105 shares, 1 point

Comments 3

Your email address will not be published.

  1. Allah ya tsine makaryaci! Wlh wlh ni ba dan PDP bane, ama wlh wanan titin dai gwamnatin Ramalan Yero ta bada shi. Kuma saida ma elrufai ya rage naira 200,000,000 a ciki na yin gadar sama don tsallakawar yara da tsuffi

You may also like