Ayi Hatarra Da Layar Yahudu Ta Shigo Nijeriya – Sheikh Sani Yahya Jingir


Sheikh Sani Yahaya Jingir

Shugaban Majalisar malamai Na ‘Kasa na ‘Kungiyar Izalah Sheikh Sani Yahaya Jingir ya gargadi musulman Nijeriya da suyi hattara da layar Yahudu ta zamani data shigo Nijeriya.

A yayin da yake gabatar da nasihar Juma’a a Masallacin ‘Yan Taya dake birnin Jos, Sheikh Jingir yace “Kasancewar kururuwar shaidan da sunan Korona virus taci nasara wajen raba mutane da yawa da tauhidin su ta hanyar hana su yin Ibadar Sallah da sauran ibada yadda Allah Ya ce don tsoron kamuwa da corona kada a mutu.

To yanzu haka Yahudawa sunyi aiki da wannan damar sun ciro wata laya, suna ruɗan ƴan boko aqeeda da sauran mutanen da suke da raunin tauhidi masu ruɗuwa da kururuwar shaiɗan suna sayan Layar ba irin ta gargajiya bane da ake rufewa da fata, tana nan tafi kobo fadi an saka sarƙa ko zare a jiki ana ratayawa a wuya.
Suka ce duk wanda ya saka layar ba zai kamu da corona ba, kuma ba zai kamu da ko wani irin virus ba ma, virus ɗin ma ba zai zo kusa da shi ba tsawon wasu meters.

Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam, yace duk wanda ya rataya laya yayi shirka. Allah Ya ce: Kace babu abinda zai same mu sai abinda Allah Ya rubuta zai same mu, Shine Majiɓincinmu, kuma ga Allah masu dogaro suke dogara. Wallahi kafirai ba zasu taba yarda da ku ba sai kun bar addininku kunbi kururuwar shaidan” A cewar Sheikh sani yahya jingir


Like it? Share with your friends!

0

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like