Atiku ya yanke shawarar Amincewa da hukuncin Kotu


Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Alh Atiku Abubakar ya bayyama amincewarsa da hukuncin da kotun Tribunal ta yanke kan kara da ya shigar.

Atiku Abubakar wanda tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PD ne zaben 2019, ya yanke wannan shawara tare da fitarwa kowa ya sani.

Mataimakin shugaban kasar, kuma dan takarar shugaban kasa ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter cikin wani dogon rubutu da ya rubuta a shafin nasa.

Mataimakin shugaban kasar ya amince da hukuncin ne domin yiwa kotu biyayya, tare da yunkurin ciyarda Nijeriya gaba.

Akwai dai jita-jita da ake yadawar cewa tsohon mataimakin shugaban kasa bai taba rashin nasara a kotu ba sai wannan karo.

Sai dai kotu ta baiwa shugaba Buhari nasara tare da amincewa dashi a matsayin wanda ya lashe zabe a shekarar 2019.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like