Atiku ya kayar da Buhari a Katsina -Maijigiri


Salisu Maijigiri shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina ya yi zargin cewa Atiku Abubakar dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 shine wanda ya lashe zaben shugaban kasa a jihar.

Muhammadu Buhari dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC wanda kuma aka bayyana ya lashe zaben ya fito ne daga jihar ta Katsina.

Jawabin na Maijigiri ya saba da sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta fitar da shi.

Sakamakon zaben da hukumar ta fitar ya nuna cewa jam’iyyar PDP ta samu kuri’a 308,056 ya yin da jam’iyyar APC ta samu kuria 1,232,133.

Da yake magana a matsayin sheda na takwas da jam’iyar PDP da Atiku suka gabatar a gaban kotun sauraron karar zaben shugaban kasa dake Abuja, Maijigiri ya yi zargin cewa sakamakon da hukumar zabe ta gabatar ba dai-dai bane.

Da yake amsa tambayoyi daga lauyoyi masu kariya ya ce sakamakon da wakilan jam’iyar suka tattara ya nuna cewa Atiku ya kayar da Buhari a Katsina.

“Mu (PDP) ne muka lashe zaben ba jam’iyar APC ba,” ya ce.

“APC ta samu kuri’a 872,000 ya yin da PDP ta samu kuria 905,000 wannan shine sakamakon zaben da muka tattara a jihar mu ba wanda yake cikin rumbun tattara sakamako na hukumar zabe ba.”

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like