Atiku ya bawa yan gudun hijirar jihar Filato tallafin naira miliyan 10


Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kuma ɗan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyar PDP ya ziyarci sansanin yan gudun hijira dake Bukuru a jihar Plataeu.

Dubban mutane ne rikicin da ake fama da shi a jihar ta Plataeu ya raba su da muhallinsu inda suke zaune a sansanin yan gudun hijira.

Ziyarar na zuwa ne dai-dai lokacin da tawagar yakin neman zaben shugaban kasa ta Atiku ke gudanar da gangamin yakin neman zabe a jihar Plataeu.

Yayin ziyarar dantakarar na jam’iyar ta PDP ya bayar da tallafin naira miliyan 10 ga mutanen dake sansanin domin rage musu radadin halin da suke ciki.

Atiku na tare da shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki da kuma sauran jiga-jigan jam’iyar ta PDP yayin ziyarar.

Ga wasu daga cikin hotunan yakin neman zabe dama ziyarar da Atiku ya kai sansanin.


Like it? Share with your friends!

1
90 shares, 1 point

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like