Atiku, Tinubu da Osinbajo sun hadu a wurin daurin aure a Abuja


Daurin auren, Isma’il Ribadu ranar Asabar a birnin tarayya Abuja , ya hada manyan yan siyasa da dama da suka fito daga jam’iyun APC da PDP.

Isma’ila ɗa ne ga Mallam Nuhu Ribadu tsohon shugaban hukumar EFCC na farko kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar ACN a zaben 2011.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci daurin auren sun hada da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da kuma Bola Ahmad Tinubu jagoran jam’iyar APC na kasa.

Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Mallam Abba kyari, gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ministan sadarwa, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami da kuma tsofaffin gwamnonin Sokoto da Ogun, Aliyu Wamakko da Ibikunle Amosun suma sun halarci taron.

An daura auren ne a masallacin Annur dake birnin tarayya,Abuja.

Ga wasu daga cikin hotunan taron daurin auren:


Like it? Share with your friends!

-1
78 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like