Atiku Bai Da Kuɗin Saye Na, Ƙuri’ata Ta Buhari Ce – Aminu Saira


Fitaccen Darktan nan na finafinan Hausa, Malam Aminu Saira, ya bayyana cewa shi ba dan siyasa ba ne kuma ba shi da jam’iyya, kawai shi masoyin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.

Fasihin Daraktan, ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsa da wakilimu ta wayar tarho. Inda ya kara da cewa babu ruwansa da wasu sabgogin ‘yan siyasa, amma yana tare da shugaba Buhari dari bisa dari.

“Duk dan Arewa mai hankali da tunani ya san irin nawuyacin halin da wasu daga cikin jihohin Arewa suka tsinci kansu a ciki kafin zuwan shugaba Buhari. Ko mu nan a Kano muna sane da hakan. Don haka ko iya wannan hujja ya isa na so Buhari saboda zaman lafiya da aka samu”, cewar Malam Aminu Saira.

Malam Aminu Saira ya kara da cewa iya rufin asiri da daukaka Allah ya huwace masa, don haka ba kudi yake bukata kafin ya so Buhari ba, kawai soyayya ce ta tsakani da Allah yake yi masa.

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like