ASUU sun Janye Yajin Aiki


A yau Laraba kungiyar malaman jami’o’in Nijeriya (ASUU) ta janye dogon yajin aikin da ta dau tsawon lokaci tana yi, har na sama da watanni Tara.

Janye yajin aikin baya rasa nasaba da yadda kungiyoyi da wasu daidaikun manyan kasar dake kishin talakawa suka matsawa gwamnatin kasar, domin ta kawo karshen yajin aikin da malam jami’o’in suke yi.

Kungiyar marubutan Arewa a kafofin sadarwar zamani “Arewa Media Writers” tana daya daga cikin kungiyar da ta bada gudumuwarta wajan kira ga gwamnatin kasar, tare da jawo hankalin gwamnati kan irin illolin da matasa suke fuskanta matukar suna zaune a gida kara zube, ba tare da sun yi karatu ba.

Kungiyar malaman jami’o’in ta umurci dukkannin daliban kasar da su hanzarta, su karkade takardunsu su koma makarantunsu domin cigaba da karatu.

Kungiyar “Arewa Media Writers” tana yiwa dukkannin daliban dake fadin kasar nan addu’a, tare da fatan kowa ya koma makaranta lafiya, domin a cigaba da karatu kamar yadda aka saba.

Daga karshe kungiyar tana kira ga al’ummar yankin Arewa, da su cigaba da yiwa yankin addu’a don samun zaman lafiya mai daurewa, dama kasar Nijeriya baki daya.


Like it? Share with your friends!

-1

Comments 4

You may also like