Arzikin Buhari ya ragu daga yadda ya ke a 2015 – Osinbajo


A daren ranar Alhamis 14 ga watan Maris ne mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce arzikin shugaban kasa Buhari ya ragu idan aka kwatanta da abinda ya mallaka a 2015.

The Nation ta ruwaito cewa mataimakin shugban kasar ya yi wannan furucin ne a wurin wata liyafar cin abinci da aka shirya a fadar Aso Villa domin karrama wadanda suka taimaka wa jam’iyyar APC neman kuri’u lokacin yakin neman zaben 2019.

Ya ce: “Na duba takardar bayyana kadarori na shugaban kasa a shekarar 2015 inda na gano na fi shi arziki kuma na ce masa, “Shugaban kasa, Na fi ka arziki sosai, wannan abin kunya ne.”
“Sai ya amsa da cewa, “Ni fa soja ne, kai kuma babban lauya ne saboda haka ya dace ka fi ni arziki.”

“Maganar gaskiya shine arzikinsa sun ragu akan yadda na gani a 2015 a yayin da na sake ganin takardan bayyana kadarorinsa.”inji Osinbajo

A yayin da ya ke tsokaci a kan zabukan da za a maimaita a wasu jihohi shida a ranar 23 ga watan Maris, Osinbajo ya bukaci ‘yan Najeriya su zabi jam’iyyar APC.

“Har yanzu ba mu kammala zabe ba.
“A ranar 23 ga watan Maris akwai zaben da za muyi a wasu jihohi shida kuma muna da ‘yan takara.
“Ba zai yiwa mu nade hannu mu ce mun gama aiki ba, har yanzu akwai sauran aiki,” a cewar Osinbajo


Like it? Share with your friends!

1
75 shares, 1 point

Comments 1

Your email address will not be published.

You may also like