APC za ta cigaba da mulki har bayan 2023 -Oshiomhole


Adams Oshiomhole, shugaban jam’iyar APC na kasa ya ce yana da yakinin cewa jam’iyar APC zata cigaba da mulki bayan shekarar 2023.

Ya yi wannan maganar ne a Abuja yayin ganawa da gwamnonin da aka zaba karkashin jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar na kasa ya shawarci mambobinta da suyi aiki tare inda ya kara da cewa akwai sauran aiki idan har ana so cigaban da aka samu ya dore.

Ya kara da cewa idan aka samu hadin kai wajen yin aiki tare tsakanin gwamnatin tarayya dana jihohi tabbas za a gudanar da ayyuka fiye da zangon farko hakan zai bawa jam’iyar ikon cigaba da mulki har bayan shekarar 2023.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like