APC Tayi Taron Jihohin Arewa Ta Tsakiya Da Nufin Shawon Kan Matsalolinta Kafin Zaben Badi
A kan haka ne ma APC ta gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a APC a jihohin Arewa Maso Tsakiyar Nigeria.

Mataimakin Shugaban APC na Nigeria mai kula da jihohin arewa maso tsakiya Alh. Mu’azu Bawa Rijau yace suna da tabbacin shawo kan duk wata ‘yar matsala kafin babban zaben na badi.

A nashi gefen Mataimakin Gwanan jihar Neja Alh. Ahmed Muhammad Ketso yace zasu tunkarin zaben tamkar yaki.

Wasu daga cikin mahalarta wannan taro da suka hada da shugaban matasan APC na jihar Neja da kuma shugaban masu fama da nakasa a APC a jihar Neja sun yi fatan za a yi tafiyar dasu dari bisa dari.

Haka zalika da dama daga cikin mahalarta wannan taro sun yi fatan gwamnatin APC karkashin Shugaban Buhari zata kammala ayyukan da ta faro a jihar Nejan ciki har da tashar Ruwan Baro.

Saurari rahoton cikin sauti:


Leave your vote

You may also like

Log In

Forgot password?

Forgot password?

Enter your account data and we will send you a link to reset your password.

Your password reset link appears to be invalid or expired.

Log in

Privacy Policy

Add to Collection

No Collections

Here you'll find all collections you've created before.

omg