APC ta yiwa PDP tayin mukami 60 domin su goyi bayan Gbajabiamila


Yan majalisar wakilai ta tarayya da aka zaba a karkashin jam’iyyar APC sun yi tayin bawa jam’iyar PDP shugabanni da mataimakan kwamitocin majalisar 60 domin su goyi bayan Femi Gbajabiamiala ya zamo shugaban majalisar.

Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Femi Gbajabiamila/Ahmad Wase, Abdulmumini Jibril Kofa shine ya bayyana haka a wata tattaunawa da yan jarida ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.

Jibrin ya ce yayan jam’iyar ta PDP sun karbi tayin da aka yi musu kuma tuni suka fara aiki tukuru wajen ganin Gbajabiamila ya zamo sabon shugaban majalisar da za a zaba.

Ya kara da cewa kawunan yan majalisar da suka fito daga jam’iyar PDP ya rabu biyu inda ya ce sun cimma matsaya ne da daya daga cikin bangarorin biyu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like