APC ta sake dage zaben fidda gwanin takarar gwamna a jihar Lagos,


Jam’iyar APC ta sake dage ranar da za ta gudanar da zaben fidda gwanin yan takarar gwamna a jihar Lagos.

Tun da farko an shirya gudanar da zaɓen ranar Lahadi amma aka dage shi ya zuwa ranar Litinin kafin daga bisani a sake matsar da zaben ya zuwa ranar Talata.

Yekini Nabena, mai rikon muƙamin kakakin jam’iyar shine ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.

A cikin sanarwar ya kara da cewa an canza ranakun gudanar da zaben a jihohin Adamawa da Enugu.

Sanarwar ta kara da cewa za ayi zaɓen fidda gwani na kato bayan kato a jihohin Enugu da Adamawa mai makon zaben na wakilai da aka amince da shi a yi tunda farko.

Za a gudanar da zabukan fidda gwanin jihohin Enugu da Adamawa a ranar 4 ga watan Oktoba.

Wannan ne dai karo na biyu da ake dage zaɓen fidda gwanin a jihar ta Lagos.

Hakan dai baya rasa nasaba da rikicin dake faruwa tsakanin gwamnan jihar Akinwumi Ambode da kuma jagoran jam’iyar na kasa Bola Ahmad Tinubu.

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like