APC ta lashe zabe a akwati dama mazabar Fayose


Ayodele Fayose tsohon gwamnan jihar Ekiti, ya gaza cin akwatin zabensa da kuma mazabarsa dake garinsu na Afao Ekiti a karamar hukumar Irepodun Ifelodun ta jihar.

Jam’iyar APC me mulkin jihar ce ta samu gagarumar nasara a kwatin, a zaben yan majalisar dokokin jihar da aka gudanar.

A akwatin Fayose dake makarantar firamare ta S.t David dantakarar jam’iyar APC a zaben,Hakeem Jamiu ya samu kuri’u 168 inda ya kayar da babban abokin takararsa, Sunday Omosilade, na jam’iyar PDP wanda ya samu kuri’u 26.

Tsohon gwamnan jihar ta Ekiti ya kasance mutumin dake gaba-gaba dake adawa da salon mulkin shugaban kasa Buhari.


Like it? Share with your friends!

-1
64 shares, -1 points

Comments 0

Your email address will not be published.

You may also like